General News

Jarumar kannywood ta haihu

TIRKASHI: Binciken Kwakwaf Ya Gano Gaskiya Kan Zargin Haihuwar Jarumar Kannywood Ba Tare da Aure BaBinciken Kwakwaf ya tabbatar da cewa, akwai wata jarumar Kannywood da ta haifi ɗa ba tare da aure ba, sai dai ba jaruma Maryam Yahaya ba ce, sabanin jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.Rahoton binciken ya bayyana cewa, sunan Maryam Yahaya an shigar da shi cikin batun ne ba tare da wata hujja ko sahihin bayani ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da suka bazu cikin sauri a shafukan sada zumunta.Binciken ya jaddada cewa, bazuwar irin waɗannan labaran ƙarya na iya ɓata suna da martabar mutane, musamman fitattun jarumai, tare da yin kira ga al’umma da su rika tantance gaskiya kafin yaɗa kowanne labari.Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa ko bayani daga jaruma Maryam Yahaya da ke nuna tana da masaniya ko alaƙa da batun da ake yaɗawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button